Home Labaru Nasarar Zabe: Dattawan Katsina Sun Kai Wa Shugaba Buhari Ziyarar Taya Murna

Nasarar Zabe: Dattawan Katsina Sun Kai Wa Shugaba Buhari Ziyarar Taya Murna

306
0
Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari, ya sha alwashin yin duk iyakar kokarin da zai yi domin rubanya ayyukan raya kasa a zangon mulkin shi na biyu.

Buhari ya bayyana haka ne, yayin da Kwamitin Amintattu na Gidauniyar Jihar Katsina su ka kai masa ziyarar taya shi murnar sake lashe zabe a karkashin jagorancin Galadiman Katsina, kuma hakimin Malumfashi Mamman Nasir, inda ya kara nuna farin cikin sa da godiya ga illahirin wadanda su ka zake zaben sa.

Ya ce irin dandazon jama’ar da su ka rika halartar gangamin yakin neman zaben sa a duk jihar da ya je, ba jama’ar da wani zai yi tunanin cewa za a iya sayen su da kudi ba ne.

Shugaba Buhari ya sake tunatar da su cewa ya taba rike shugabancin Gidauniyar Jihar Katsina a tsawon shekaru 17, inda a lokacin gidauniyar ta gudanar da gagarumin aikin tallafa wa bangaren ilmi da kiwon lafiya da kuma aikin noma, musamman ga masu karamin karfi.

Galadiman Katsina Mamman Nasir, ya ce Gidauniyar Jihar Katsina na kara godiya ga Allah da ya sake ba Buhari damar sake shugabancin Nijeriya a shekaru hudu masu zuwa.