Ƙungiyar malaman Jami’oi ta Najeriya ASUU, ta ba gwamnatin Majeriya sabon wa’adin kwana 14, bayan karewar wa’adin kwana 21 da tun a farko ta ba gwamnati,
Domin warware matsalolin da ke tsakanin su ko kuma ta tsunduma yajin aiki.
Shugaban ƙungiyar Emmanuel Osodeke ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar,
inda ya ce jan ƙafar da gwamnati ke yi game da lamarin na ƙara mai da hannun agogo baya, wajen sha’anin gudanarwar jami’oin gwamnati a ƙasa.
ASUU ta ce kar al’umma su yi kuka da ita idan ta tsunduma yajin aiki, domin a cewar ta matsalolin da ake samu a yanzu game da matsalolin su daga ɓangaren gwamnati ne.
Daga cikin buƙatun ƙungiyar ta ASUU, akwai buƙukatar kammala cimma matsayar kan yarjejeniyar su da gwamnati ta shekarar 2009 karkashin shawarwarin da kwamitin Nimi Briggs ya samar a shekarar 2021,
Da kuma biyan ‘ya’yan ta albashin su da aka rike sakamakon yajin aikin wata 8 da suka yi a shekarar 2022.
Sauran sun haɗa da, samar da tsarin biyan malamai da zai maye gurbin na IPPIS da gwamnatin Najeriya ke amfani da shi wajen biyan ma’aikata albashi.