Home Labarun Ketare Goguwa: Arewacin Florida Ta Gigita

Goguwa: Arewacin Florida Ta Gigita

2
0
108040562 1727555635887 gettyimages 2174219458 AFP 36HC8ER
108040562 1727555635887 gettyimages 2174219458 AFP 36HC8ER

Wata guguwa mai ƙarfin gaske da aka yi wa laƙabi da Hurricane Helene, ta afka wa arewacin jihar Florida ta ƙasar Amurka inda ta taho da iskar da gudun ta ya kai kilomita ɗari biyu da ashirin da biyar.

Tun da farko dai, gwamnan jihar Ron De-sanctis ya ce ta riga ta yi sanadiyar mutuwar mtum ɗaya, kuma ya gargaɗi mazauna jihar su ɗauki matakan kiyaye kan su daga guguwar.

Ya ƙara kira ga jama’a su kula da irin bishiyoyin da ke kusa da su, saboda a cewar sa guguwa ce mai ƙarfin gaske kuma yayin da take ƙara kusantar jihar bishiyoyi da dama ne za su riƙa faɗuwa.

Ya kuma shawarci mazauna jihar su zauna cikin gidajen su har sai guguwar ta wuce.

Leave a Reply