Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta tabbatar da mutum 67 ne suka kamu da cutar kyandar biri daga cikin mutum dubu 1 da 31 da aka yi fargabar sun kamu da cutar a jihohi 23, ciki har da nan babban birnin tarayya Abuja.
NCDC ta ce jihar Akwa-Ibom da Enugu kowacce na da mutum takwas da suka kamu, sai Bayelsa da ke da shida, sai Cross-River mai biyar, da kuma sauran mutum 40 da suka watsu a sauran jihohi 19.
Shugaban hukumar ta NCDC, Jide Idris ya ce hukumar ta ƙara zage damtse domin yaƙi da yaɗuwar cutar, ya kuma ce suna ƙara inganta ɗakunan gwaje-gwajen su a faɗin ƙasa domin tabbatar da cewa ba sai an yi ta yin jigila domin gwajin cutar ba.
Kawo yanzun dai rahotanni sun tabbatar da cewa ƙasashe 13 ne suke fama da cutar kyandar biri a Afirka bayan ƙasar Guinea ta sanar da mutum na farko da ya kamu.