Yayin da tasirin wasu a nahiyar ke fuskantar barazana – misali Faransa da sauran ƙasashen Tarayyar Turai waɗanda hukumomin soji na Sahel suka juya wa baya, da kuma tayin sojojin haya na Rasha da wasu gwamnatocin Afrika aminan ƙasashen yammaci ba su yi amnna ba – China ta kasance ƴar ba ruwanmu.
Wakilai daga ƙasashe 50 na sassan Afrika sun amince da gayyatar Beijing a taron China da Afrika a wannan makon.
Shugabannin ƙasashe da dama suka halarci taron – ciki har da António Guterres, shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya.
Cikinsu akwai shugaban Congo-Brazzaville Denis Sassou- Nguesso da kuma sabon shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye – wanda aka ba sahun gaba kusa da shugaba Xi Jinping a hoto tsakanin shugabannin da suka halarci taron.
Ga gwamnatocin Afrika da ke fuskantar matsin lamba daga siyasar duniya kan fitowa su bayyana inda suka dogara, China yanzu za ta kasance babbar aminiya ba tare da tsangwama ba daga aminan Rasha da kuma ƙasashen da ke ƙawance da Turai da kuma Amurka.
Beijing na son ƙarfafa tattalin arzikinta da kuma neman albarkatun ƙasa, tare da tayin tallafin samar da ci gaba da kuma gina abubuwan more rayuwa a Afrika.