Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede ya bayar da umarnin a gaggauta bincike kan zargin cin hanci da rashawa da Idris Okuneye wanda aka fi sani da Bobrisky ya yi a kan wasu jami’an hukumar.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Bobrisky ya bayyana a wani faifan bidiyo inda ya zargi wasu jami’an hukumar waɗanda ba bayyana sunan su ba sun nemi Naira miliyan 15 daga wajen sa domin dakatar da binciken da ake yi a kan sa kafin a tura shi gidan yari.
Wannan ya sa shugaban hukumar ya kafa kwamitin bincike domin tabbatar da gaskiya ko akasin zargin.
EFCC ta kuma gayyaci Okuneye zuwa ofishin ta na Legas domin taimakawa wajen gudanar da binciken.
A wata sanarwa da mai Magana dayawun hukumar, Dele Oyewale ya fitar, ya tabbatar da cewa za a bincika zargin, sannan za a fitar da sakamako idan an kammala binciken.