Gwamnatin jihar Kano ta sanar da ranar Lahadi, 15 ga Satumba, 2024, a matsayin sabuwar ranar da za a’ koma makaratun kwana na sakandare da kuma makarantun firamare na gwamnati da masu zaman kan su a zangon farko na shekarar 2024/2025.
Hakazalika ɗalibai a makarantun je-ka-ka-dawo a fadin jihar za su koma ranar Litinin 16 ga Satumba, 2024.
A wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar, Balarabe Abdullahi Kiru ya fitar, gwamnatin jihar ta buƙaci iyaye su yi la’akari da sabon ranar da za a koma makarantar domin tabbatar da cikakken bin doka da oda.
Sanarwar ta kuma shawarci ɗalibai su guji shiga da abubuwan da ba a yarda da su ba makarantun su da kuma ya saɓawa doka, kamar irin su wuƙaƙe ko reza, kuma su tabbatar da bin doka.
Sanarwar ta jaddada ƙudirin gwamnatin jihar na ganin kowane yaro ya samu ilimi mai inganci.