Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta kama wasu miyagu mutane 280 da ke safarar kwayoyi a jihar Kano.
Kwamandan hukumar na jihar Ibrahim Abdul ya bayyana haka a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a kan al’amurran da suka shafi yaki da tu’ammuli da miyagun kwayoyi a watan Maris.
Abdul ya ce hukumar ta samu nasarar kama ‘yan hana ruwa gudu a jihar, tun bayan kaddamar shirin sharar miyagu domin kawo karshen tu’ammuli da miyagun kwayoyi a jihar.
Kwamanda ya kara da cewa, hukumar ta kuma samu nasarar kama miyagun kwayoyi da suka kai nauyin kilogram miliyan 1 da dubu dari 248 da dari 775 na nau’ikan kwayoyi daban-daban da suka hadar da taba wiwi da kuma kwayoyin magani masu sa maye da kuma gushewar hankali.