Fasinjoji a faɗin kasar nan sun shiga tasku, bayan da kamfanonin jiragen sama suka dakatar da zirga- zirga.
Hakan ya jefa mutane da dama cikin halin rashin tabbas, duba da ƙarancin jiragen da ke zirga-zirga, musamman daga Legas zuwa Abuja da kuma Abuja zuwa Legas.
Fasinjoji da dama ba su samu damar yin tafiya ba a sakamakon wannan matsala.
Jirgin Max Air na ƙarfe 6 na yamma daga Legas zuwa Abuja ya cika gaba ɗaya amma abun mamaki bai tashi ba.
Haka kuma, jiragen Air Peace na ƙarfe 6:30 da 8:30 na yamma sun bayyana cewar ba su da sauran kujeru a ƙasa.
Wani ma’aikacin jirgi da ya nemi a sakaya sunansa ya ƙara da cewa kamfanonin jiragen sama na rage yawan tashi don kauce wa matsaloli.
Masanin harkokin sufurin jiragen sama, Mista Olumide Ohunayo, ya ce wannan yanayi ba zai rasa nasaba da sabbin dokokin kare haƙƙin masu amfani da jiragen sama ba.