Wani sabon ƙalubale ya bullo wa jama’a sama da miliyan 2 da aka haƙiƙance cewa ambaliyar birnin Maiduguri a arewa maso gabashin Najeriya ta tagayyara.
Mazauna birnin na Maiduguri sun ce suna fuskantar matsananciyar tsada daga masu kwale-kwale a daidai lokacin da buƙatar su ke ƙaruwa a kusan galibin birnin da ambaliya ta mamaye.
A makon da ya gabata da ambaliyar ta afku masu kwale-kwale na yin aikin ceto ba tare da biyan ko sisi ba amma a yanzu lamarin ya sauya, sakamakon ababan hawa basa iya kaiwa wurare da dama a birnin.
Baba Ali-Maina ɗan shekara 51 dake da yara 4 ya bayyana ƙaduwar sa bayan ya biya dubu 70 domin a fitar da wasu kayan wuta da kuma na’urar girki ta gas daga gidan sa da ruwa ya mamaye,
domin ya gwammace biyan wannan kuɗin maimakon barin kayan sa saboda gudun kada barayi da suke shiga su sace.
Sai dai wani matuƙin kwale-kwale Muhammad Yusuf ya ce har yanzu yana aiki kyauta amma kuma yaran da suke tayashi aiki ba ƴaƴan sa bane don haka yana biyan su.