INEC ta ce ta samu bukatu da dama daga kungiyoyi daban-daban a fadin kasa, suna neman su yi wa wakilan su kiranye a majalisun tarayya da na jihohi.
Dokar zaben Najeriya dai ta ba masu zabe damar janye wakilan su a majalisu idan har suka kai wani adadi.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar ta fitar da sabbin Dokoki da Ka’idoji da aka gyara don janye ‘yan majalisun tarayya da na jihohi, har da kansiloli a Majalisar Kananan Hukumomin Babban Birnin Tarayya Abuja.
Kwamishina na kasa kuma Shugaban Kwamitin Bayar da Bayani da Ilimin Zabe na INEC Mista Sam Olumekun, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa bayan taron shugabannin hukumar.
Ya ce an yanke wannan shawarar ce tare da sake duba shirin karshe don zaben gwamna na jihar Edo wanda zai gudana ranar Asabar mai zuwa.