Home Labaru Kasuwanci Sufuri Da Abinci: CBN Ya Ce Man Fetur Na Dangote Zai Kawo...

Sufuri Da Abinci: CBN Ya Ce Man Fetur Na Dangote Zai Kawo Saukin Farashi

17
0
A section of the Dangote refinery 1
A section of the Dangote refinery 1

Babban Bankin Najeriya CBN ya ce fara jigilar man fetur daga matatar man fetur ta Dangote zai rage farashin sufuri da abinci a Najeriya.

Gwamnan babban bankin Olayemi Cardoso ya bayyana haka a hirar sa da manema labarai a ranar Talata, bayan taron kwamitin tsare-tsaren harkokin kuɗi wato MPC a Abuja.

Ya ce kwamitin ya nuna ƙwarin gwiwar cewa samar da man fetur daga matatar man fetur ta Dangote zai taimaka wajen rage farashin kayan masarufi.

Ya ce haka kuma zai taimaka wajen rage buƙatun kuɗaɗen ƙasashen waje da ake yi domin shigo da man fetur Najeriya.

A watan Satumba ne babban kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL, ya fara jigilar man fetur karon farko daga matatar man Dangote

Leave a Reply