Home Labaru Kimiyya NIMET Ta Yi Hasashen Samun Zazzafar Rana A Jihohin Kano, Katsina Da...

NIMET Ta Yi Hasashen Samun Zazzafar Rana A Jihohin Kano, Katsina Da Sokoto

127
0

Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya NiMet, ta yi hasashen
samun hasken rana da gajimare daga ranar Litinin zuwa
Laraba a fadin Nijeriya.

An dai fitar da hasashen yanayin ne a ranar Lahadin da ta gabata a Abuja, inda hasashen ya nuna akwai yiwuwar samun tsawa a jihohin Taraba da Adamawa da Sokoto da Zamfara da Kebbi da kuma Kaduna.

Hukumar ta kara da cewa, ana kuma iya samun tsawa a wasu sassan jihohin Kaduna da Taraba da Adamawa da Bauchi da Gombe da Katsina da Borno da Yobe da kuma Kano.

Kamar yadda kafar yada labarai ta hukumar ta ruwaito, ana sa ran zazzafar rana tare da gizagizai a yankin Arewa ranar Talata 11 ga watan Yuli, inda ake sa ran za a yi tsawa mai karfin gaske a sassan jihohin Jigawa da Kaduna da Kano da Katsina da Zamfara da Sokoto da Kebbi da Taraba da kuma Adamawa.

Leave a Reply