Home Labaru Ilimi An Sake Mayar Da Jami’ar Sa’adatu Rimi Zuwa Kwaleji

An Sake Mayar Da Jami’ar Sa’adatu Rimi Zuwa Kwaleji

34
0
Screenshot 20240228 075959 Chrome
Screenshot 20240228 075959 Chrome

Majalisar zartarwar Jihar Kano ta amince da mayar da Jami’ar ilimi ta Sa’adatu Rimi zuwa Kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi, tare da ci gaba da bayar da takardun digiri.

An yanke wannan hukuncin ne a zaman majalisar na 18, bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan irin sauyin da mayar da ita a jami’a zai haifar da suka haɗa da yiwuwar rasa kwararrun malaman jami’a da kuma rikicin albashi.

Kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Baba Halilu Dantiye, ya bayyana cewa jihar ta zaɓi tsarin “Dual Mode”, wanda zai bai wa cibiyar damar ci gaba da zama kwaleji tare da bayar da shirye-shiryen digiri,\

matakin da ya samo asali domin samar da tsari mai ɗorewa ga ci gaban makarantar.

Ya bayyana cewa an tabbatar wa ɗalibai wannan sauyinn ba zai shafi karatun su ba, kuma kwalejin za ta ci gaba da shirye-shiryen ta na farko da sabbin digiri sannan Bugu da ƙari,

za a adana takardun shaidar jami’ar don amfani a nan gaba, tare da samar da damar sauya alkibla idan buƙatar hakan ta taso.

Hukumar kula da jami’o’i ta ƙasa NCC ce dai ta amincewa Kwalejin komawa jami’a a watan Fabrairun shekarar 2023 lokacin mulkin Abdullahi Umar Ganduje.

Leave a Reply