United na farautar ɗan wasan Ingila, Jarrad Branthwaite, wanda aka kiyasta kudinsa ya kai fam miliyan 60 zuwa 70.
Aston Villa na son sayen ɗan wasan Chelsea mai shekara 24 da ke buga tsakiya, Conor Gallagher.
Manchester City na duba yiwuwar sayen mai tsaron raga a ƙungiyar Werder Bremen ta Jamus ɗan shekara 28, Michael Zetterer.
Liverpool na shirin gabatar da tayi kan ɗan wasan Netherlands mai shekara 20, Conor Bradley.
Manchester United na duba yiwuwar musayan ‘yan wasa tsakanin Mason Greenwood da kuma ɗan wasan Atletico Madrid, mai shekara 24, Joao Felix.