Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da mutuwar jami’an ta biyar a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a garin Karfi da ke karamar hukumar Kura a jihar.
Kakakin rundunar ‘yansandan Kano, Abdullahi Kiyawa, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata, ya ce, wasu jami’an ‘yan sanda 11 sun samu raunuka a hadarin.
Ya ce hatsarin ya afku ne a kauyen Karfi da ke karamar hukumar Kura yayin da jami’an ke dawowa cikin garin Kano daga wani aiki da aka tura su a hukumance.
Ya ce jami’ai 5 ne suka mutu nan take yayin da wasu 11 kuma suka samu raunuka daban-daban aka garzaya da su asibitin kwararru na Murtala Mohammed inda a yanzu haka suke samun kulawar likitoci.