Masanin tattalin arziki Dakta Kasum Garba Kurfi ya ce akwai alfanu sosai dangane da samun matatar man fetur ta Dangote da ta fara aiki a Najeriya.
Dr. Kasum Kurfi wanda ya bayyana haka, yace irin kayayyakin da matatar Dangote za ta samar ga jama’ar Najeriya su na da matukar yawa wadanda a baya dole sai an je kasashen waje kafin a sayo su.
Masanin ya ce baya ga man dizil da iskar gas na girki da kuma na masana’antu da man jiragen sama, sabuwar matatar za ta samar da sinadarin robobin da ake amfani da su wajen yin kayayyakin da ake yi da roba da kuma takin zamani da maganin kwari da maganin sauro da man shafawa da wasu ayyuka daban daban.
Kasum Kurfi ya kuma ce kusan kashi 70 na ma’aikatan dake aiki a matatar man Dangote ‘yan Najeriya ne, wanda hakan ba karamin taimakawa zai yi wajen rage matsalar rashin ayyukan yi ba da kuma da bunkasa tattalin arzikin kasa.
Masanin ya ce fara aikin matatar kuma za ta bude kofa ga kasashen duniya su dinga zuwa Najeriya domin sayen wadannan kayayyaki da kudaden wajen da ake matukar bukatar su.
Tuni matatar ta Dangote ta fara sayar da man jiragen sama da kuma dizil a kasashen Turai da kuma Amurka, ya yin da a karshen makon da ya gabata, ta fara sayar da man fetur a cikin gida.