Home Labarai ‘Yan Sanda Sun Tsinci Gawa Cikin Makarantar Islamiyya A Jigawa

‘Yan Sanda Sun Tsinci Gawa Cikin Makarantar Islamiyya A Jigawa

28
0
Rataya
Rataya

An tsinci gawar wani mutum ɗan shekara 40, Jibrin Adamu, a cikin ajin wata makarantar Islamiyya a Karamar Hukumar Kiyawa a Jihar Jigawa.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam, ya ce ’yan sanda sun gano gawar a rataye a saman silin na makarantar Miftahul Khairat Islamiyya da ke unguwar Gurdiba.

A cewar sa, jami’in ’yan sandan shiyya na Kiyawa da tawagar sa ne suka gano gawar a lokacin da suka isa wurin bayan sun samu rahoton.

DSP Lawan Shiisu Adam ya ce rundunar ’yan sandan ta kaddamar da bincike kan lamarin da ya faru a ranar Talata, 19 ga Satumba, 2024, ya ce marigayin,

yana da tarihin matsalar tabin hankali kuma a wasu lokuta yana barin gida na tsawon kwanaki.

Ya ce a ranar mutuwar sa an gan shi yana dibar ruwa a kusa da makarantar inda daga bisani aka tsinci gawar sa rataye a saman rufi.

Ya ce an kai gawar babban asibitin Dutse, inda aka tabbatar da mutuwar, kuma daga baya aka mika gawar ga ’yan uwan sa domin yi masa jana’iza.

Shiisu ya bayyana cewa rundunar ’yan sandan jihar Jigawa tana kira ga duk wanda yake da labarin rasuwar Adamu ya taimaka mata.

Leave a Reply