A halin da ake ciki dai ana ci gaba da rade-radin cewa shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu zai sauke wasu ministocin sa da ba su yi abun a zo a gani ba,
wanda aka ce an fara maganar ce a zaman majalisar zartaswa ta tarayya da shugaban kasan ya jagoranta a ranar Litinin.
Rahotanni da dama sun nuna cewa Shugaba Tinubu na shirin yin wasu sauye-sauye ne nan ba da jimawa ba, bayan ya yi barazanar sallamar wasu ministocin sa da ba su taka rawar gani ba,
amma dai shugaban kasan bai tabbatar da takamammen lokaci ko yadda sauyin zai gudana ba.
A taron majalisar zartarwar, sakataren gwamnatin tarayya, sanata George Akume, ya jinjina wa shugaba Tinubu kan rawar da ya taka wajen tabbatar da sahihin zaɓe a Jihar Edo,
ya kuma taya jam’iyyar APC murna kan nasarar da suka samu a zaɓen Sanata da aka gudanar kwanan nan a jihar.
Geoge Akume, ya kuma sanar da majalisar game da rasuwar tsohuwar Ministar Harkokin Mata, Salome Jankada, wadda ta rasu a ranar 27 ga watan Agusta,
inda majalisar ta yi ta’aziyya tare da girmamawa ga tsohuwar ministar.
Manyan jami’an gwamnati irin su mai ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, da wasu ministoci ne suka halarci taron.