Home Labaru Ciyar Da Dalibai: ‘Yan Firamare Na Cin Shanu 594 Da Kaji 148,000...

Ciyar Da Dalibai: ‘Yan Firamare Na Cin Shanu 594 Da Kaji 148,000 Da Kwayaye Miliyan 6.8 – Osinbajo

297
0
Farfesa Yemi Osinbajo, Mataimakin Shugaban Kasa
Farfesa Yemi Osinbajo, Mataimakin Shugaban Kasa

Gwamnatin tarayya, ta na ciyar da daliban makarantun Fimare abinci daban-daban a karkashin tsarin jam’iyyar APC na ciyar da dalibai kamar yadda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana.

Osinbajo, ya ce gwamnati na ciyar da dalibai da shanu 594, da kaji dubu dari da arba’in da takwas, da kwayaye miliyan shida da dubu dari takwas da kuma Ton tamanin da uku da kifi a kowane mako.

Yemi Osinbajo ya bayyana haka ne, yayin da ya ke jawabi a wajen bikin yaye daliban jami’ar Legas karo na 50.

Ya ce dalibai miliyan tara da dubu dari uku da dari takwas da casa’in da biyu ne su ke cin gajiyar tsarin a makarantu dubu arba’in da dari takwas da talatin da bakwai a jahohi ashirin da shida.

Mataimakin shugaban kasar ya cigaba da cewa, sun dauki ma’aikata masu dafa abinci dubu casa’in da biyar da dari hudu da ashirin da biyu a karkashin tsarin, sannan akwai kananan manoma sama da dubu dari da gwamnati ke sayen kayan hadin abinci daga wajen su.

Leave a Reply