Ɗan wasan Real Madrid Kylian Mbappe zai yi jinya kamar yadda Real Madrid ta samar.
Ɗan kasar Faransa, wanda ya koma Real kan fara kakar bana daga Paris St Germain ya ci ƙwallo a La Liga da suka doke Deportivo Alaves 3-2 ranar Talata.
An sauya Mbappe daga karawar sauran minti 10 a tashi daga babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Bayan da aka tashi daga wasan ne, Carlo Ancelotti ya sanar cewar yana cikin koshin lafiya, Mbappe ne ya bukaci a canja shi, saboda kada a samu matsala.
To sai dai ranar Laraba Real Madrid ta sanar cewar ɗan wasan mai shekara 25 na ɗauke da rauni, sakamakon gwaje-gwajen da ta yi masa.
Real Madrid za ta je gidan Atletico Madrid a wasan hamayya a La Liga ranar Lahadi daga nan ta fuskanci Lille a Champions League.
Haka kuma Real Madrid za ta kece raini da Villareal a La Liga daga nan a shiga watan Oktoba.
Mbappe ya ci ƙwallo shida a karawa bakwai da ya yiwa Real Madrid a kakar nan, kafin ya ji rauni, sai dai ba a fayyace kwanakin da zai yi jinya ba.