Shugaban kungiyar Hezbollah da ke Lebanon Hassan Nasrallah ya ce babu wani abu da Isra’ila za ta yi da zai sa su daina kai mata hari yankin arewaci inda Yahudawa ‘yan kama wuri zauna suke.
Jagoran yana mayar da martani ne a wani jawabi da ya yi a ranar Alhamis da daddare bayan hare-haren da kungiyar sa ke zargin Isra’ila ta kai ta na’urorin sadarwa da Hezbollah ke amfani da su a Lebanon.
Yayin da yake jawabin, Isra’ila ta ce jiragen saman ta na yaki sun kai hari kan makaman harba roka sama da dari daya na kungiyar Hezbollah da sauran wuraren da ta kira da masu kai hari da suka hada da wani rumbun makamai a kudancin Lebanon.
Rundunar sojin Isra’ila ta ce, ana dab da shirin kai hare-haren rokar ne kan Isra’ila lokacin da jiragen nata suka kai harin.
Ba a dai sani ba ko akwai wasu mutane da hare-haren suka ritsa da su.