Home Labaru Nadin Mukamai: ‘Yan Damfara Na Gab Da Damfarar Manyan Jami’an Gwamnati –...

Nadin Mukamai: ‘Yan Damfara Na Gab Da Damfarar Manyan Jami’an Gwamnati – DSS

341
0

Yayin da Shugaba Muhammadu Buhari ke yunkurin kafa sabuwar majalisa ta hanyar nade-naden wasu sabbin ministoci, hukumar tsaro ta farin kaya DSS, ta yi gargadi a kan yunkurin da wasu ‘yan rufa ido ke yi domin damfarar manyan jami’an gwamnati makudan kudade.

A cikin wata sanarwa mai dauke sa hannun kakakin ta Peter Afunanya, hukumar ta ce yunkurin da ‘yan damfarar ke yi wani sabon salo ne na damfara da aka shirya musamman a kan manyan jami’an gwamnati.

Hukumar DSS dai ta na jan hankalin jama’a, musamman shugabannin hukumomin gwamnati a kan sabon salon damfara a da aka shirya musamman a kan su.

Bincike ya nuna cewa, ‘yan damfarar su na amfani da sunan wasu shugabannin hukumomi wajen damfarar makudan kudade.

Hukumar ta kuma bukaci mutane su sanar da ita cikin gaugawa da zarar sun ga wani abu da ya yi kama da na ‘yan damfara.

Leave a Reply