Home Labaru Hangen Nesa: Siyasar Kabilanci Ke Lalata Nijeriya – Jega Da Nnamani

Hangen Nesa: Siyasar Kabilanci Ke Lalata Nijeriya – Jega Da Nnamani

319
0
Farfesa Attahiru Jega, Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa
Farfesa Attahiru Jega, Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa

Tsohon shugaban majalisar dattawa Ken Nnamani, da tsohon shugaban hukumar zabe Farfesa Attahiru Jega, sun bayyana siyasar kabilanci a matsayin abin da ke kashe Nijeriya.

Shugabannin biyu dai sun bayyana haka ne, a wajen taron yaye daliban da su ka kammala karatu a jami’ar Nnamdi Azikiwe da ke Awka a jihar Anambra.

Yayin da ya ke gabatar da jawabi a wajen taron, Nnamani ya ce ‘yan siyasar Nijeriya sun gaza daukar darasi daga kurakuren baya na siyasar kabilanci, wanda ya yi sanadiyyar lalacewar Nijeriya.

A na shi bangaren, Farfesa Attahiru Jega ya ce, gazawar ‘yan Nijeriya wajen guje ma siyasar kabilanci, ta kasance babbar matsalar da hadin kan kasa ke fuskanta, musamman ta yadda harkar siyasar Nijeriya to koma hannun mutanen marasa kishin kasa.

Ya ce lokaci ya yi na fara bada gudumuwa ga cigaban siyasar Nijeriya ba tare da barin ta a hannun wadanda su ka rasa alkibla da martaba ba.