Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha, ya ce abin da ya yi gudu a jam’iyyar PDP bai kai kashi daya cikin goma na rashin mutuncin da aka yi ma shi a jam’iyyar APC ba.
Rochas Okorocha dai, ya na fama da matsalar hana bayyana sakamakon zaben sa, da kuma ba shi takardar shaidar lashe zaben kujerar sanata.
Ya kuma zargi shugaban jam’iyyar APC da wasu shugabannin jam’iyyar da bai ambaci sunayen su ba, cewa su na hada baki da hukumar zabe domin a kashe kaifin alkiblar siyasar sa.
Idan dai ba a manta ba, hukumar zabe ta ce Okorocha ne ya lashe zaben sanata na mazabar Imo ta Kudu, sai dai a cikin kankaninn lokaci kwamishinan zabe na jihar ya nuna cewa tilasta shi aka yi ya sanar cewa Okorocha ne ya lashe zaben.