Home Labaru Korafi: Kananan Hukumomi Sun Zargi Gwamnatin Zamfara Da Tauye Masu Kudade

Korafi: Kananan Hukumomi Sun Zargi Gwamnatin Zamfara Da Tauye Masu Kudade

296
0
Bello Muhammad Matawalle, Gwamnan Jihar Zamfara
Bello Muhammad Matawalle, Gwamnan Jihar Zamfara

Kungiyar shugabannin kananan hukumomi reshen jihar Zamfara ALGON, ta ce gwamnatin jihar Zamfara na tauye masu kudin da aka tura masu daga gwamnatin tarayya, duk da umurnin da shugaban kasa ya bada cewa a hannunta wa kananan huumomi kudaden su.

Mai magana da yawun kungiyar kuma shugaban karamar hukumar Maradun Ahmed Abubakar, ya ce gwamnatin jihar Zamfara ta saba wa umurnin da shugaban kasa ya bada.

Ya ce sun yi mamaki matuka da wakilan gwamnati su ka gaya masu cewa baya ga kudaden da aka saba badawa na albashin ma’aikata da sauran kudaden da ya wajabta a cire, an ba su umurnin su ba kowane shugaban karamar hukuma Naira miliyan biyar da zai gudanar da mulkin karamar hukumar tsawon kwanaki 30 masu zuwa.

Ya ce duk shugabannin kananan hukumomin da aka zaba a karkashin jam’iyyar APC za su kai gwamnatin jihar kara idan ta sake yin kokarin hana su kudaden su.

Da ya ke maida martani game da zargin, daraktan yada labarai na gwamnatin jihar Yusuf Idris, ya ce an gayyaci shugabannin kananan hukumomi zuwa wajen taron duba asusun ajiya na hadaka da ake yi duk wata, amma su ka ki halartar taron.

Leave a Reply