Home Labaru Wata Sabuwa: ‘Yan Shi’a Sun Harbi ‘Yan Sanda 3 A Majalisar Dokoki

Wata Sabuwa: ‘Yan Shi’a Sun Harbi ‘Yan Sanda 3 A Majalisar Dokoki

692
0

Rahotanni ne cewa, ‘yan kungiyar Shi’a sun harbi wasu jami’an ‘yan sanda da ke bakin aiki a majalisar dokoki ta tarayya, Lamarin ya haddasa tashin hankali a cikin harabar majalisar da ke Abuja.

Wata majiya ta ce an yi gaugawar daukar daya daga cikin jami’an ‘yan sandan zuwa asibitin majalisar dokoki da misalin karfe 1:55 na rana.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, lamarin ya afku ne a lokacin da masu zanga-zangar su ka yi kokarin kutsa kai cikin majalisar da karfin tuwo.

Haka kuma, ‘yan Shi’ar sun cinna wa wasu motoci da aka ajiye kusa da mashigin majalisar wuta, yayin da aka karo jami’an tsaro zuwa wajen da lamarin ke faruwa, inda da zuwan jami’an ‘yan sanda su ka rufe mashigin majalisar, yayin da karar harbin bindigogi a sama ta karade ko ina.

Motar Police Da Yan Shi’ite suka Bata

Leave a Reply