Sakataren gwamnatin Tarayya Boss Mustapha, ya ce akwai wadanda su ka sha gaban shi ta fuskar cancantar hawa kujerar da ya ke a kai yanzu.
Idan dai ba a manta ba, a ranar Juma’ar da ta gabata ne shugaban kasa Buhari ya sabunta nadin mukamin sakataren gwamnatin Tarayya da kuma Abba Kyari a matsayin shugaban ma’aikata na fadar gwamnatin sa.
Boss Mustapha ya bada bayanin yadda ya samu kwarewa yayin sauke nauyin mukamin sa na kujerar sakataren gwamnatin Tarayya, ya na mai godiya ga Allah da kuma shugaba Buhari da ya amince da sahihancin sa.
A karshe ya bada tabbacin cewa zai jajirce wajen gudanar da aiki tukuru yayin sauke nauyin da ya rataya a wuyan sa fiye da yadda ya yi a wa’adin sa na farko.