Home Labaru Hukumar Ƙidaya Ta Fara Aika Gayyatar Horarwa Ga Ma’Aikatanta

Hukumar Ƙidaya Ta Fara Aika Gayyatar Horarwa Ga Ma’Aikatanta

75
0

Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa ta fara aika saƙon gayyata, zuwa ga
masu ƙidayar jama’a da masu sa ido domin horar da
ma’aikatan wucin gadi.

A wata Sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce hukumar gudanarwa ta fara aikewa da takardar gayyatar horo ga ma’aikatan da aka amince da su, domin horar da matakin ƙaramar hukumar da aka tsara zai fara a ranar 11 ga Afrilu na shekara ta 2023.

Dangane da saƙon da aka aika a gayyatar, hukumar NPC ta ce za a gudanar da matakin farko na horar da ma’aikata daga ranar 11 zuwa 17 ga watan Afrilu.

Gayyatar, ta kuma ƙunshi cibiyoyin horar da masu ƙidaya da masu kula da masu halartar ƙaramar hukumar su.

Leave a Reply