
Gwamnatin tarayya ta kalubalanci dan takarar shugaban kasa
na jam’iyyar labour Peter Obi, ya fito ya fayyace matsayin sa
dangane da sakon sautin da aka yada na tattaunawar da ta
gudana tsakanin shi da shugaban babbar Mujami’ar ‘Living
Faith’ Bishop David Oyedepo.
Ministan yada labarai Lai Mohammed ya kalubalanci Peter Obi, yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a birnin London, inda ya ce ya kamata ya yi wa jama’a bayani a kan abin da ya ke nufi da cewa sautin da aka nadi muryar sa da ta Bishop Oyedepo na karya ne.
A farkon watan Afrilu ne, aka wayi gari da yaduwar sakon sautin da ke dauke da tattaunawar Peter Obi da Bishop Oyedepo, wanda a cikin sa aka jiyo muryar Peter Obi ya na neman taimakon Bishop Oyedepo ya ja hankalin mabiya addinin Kirista su goyi bayan takarar da ya ke yi, inda ya kuma bayyana zaben da ake tunkara a matsayin yakin addini.
Sai dai daga baya Peter Obi ya yi watsi da sautin muryoyin, tare da bayyana shi a matsayin karyar da aka shirya domin bata ma shi suna.
You must log in to post a comment.