Home Labarai Karancin Kudi: Da Sauran Rina A Kaba — Masana

Karancin Kudi: Da Sauran Rina A Kaba — Masana

1
0

Yayin da ‘yan Nijeriya ke kokawa a kan wahalhalun rayuwa
sakamakon karancin Naira, kwararru da masana harkokin kudi
sun shawarci jama’a su jajirce domin tunkarar karin matsin da
lamarin ya haifar.

Duk da tabbacin da Babban Bankin Nijeriya ya bada na saukaka matsalar karancin kudi, masana tattalin arziki da kwararru da masu sharhi a kan harkokin kudi, sun ce ‘yan Nijeriya za su cigaba da rayuwa cikin karancin kudi na tsawon lokaci idan ba a samu manyan sauye-sauye a kan yadda mahukuntan Bankin su ke tunkarar lamarin ba.

Idan za a tunawa, Kungiyar Kwadago ta Kasa ta tilasta wa bankin CBN sauka daga dokin na ki, inda ta yi barazanar durkusar da tattalin arzikin Nijeriya idan ba a samu ingantuwar zagayawar kudade a hannun jama’a ba.

Matakin dai ya zo ne bayan makonni da fara bin wani bangare na hukuncin Kotun Koli da ya tsawaita amfani da tsofaffin takardun kudin zuwa watan Disamba, sai dai yawan kudin da bankunan su ka samu ya yi matukar nesa da abin da tattalin arzikin kasa ke bukata domin yaukaka shi gaba daya.