Home Ilimi Gwamnatin Bauchi Ta Ja Kunnen Masu Wa’Azi Kan Amfani Da Kalaman Tunzura...

Gwamnatin Bauchi Ta Ja Kunnen Masu Wa’Azi Kan Amfani Da Kalaman Tunzura Jama’a

114
0

Gwamnatin Jihar Bauchi, ta ce ba za ta lamunci kalaman
tunzura jama’a daga duk wani mai wa’azi a fadin jihar ba.

Sakataren gwamnatin jihar Ibrahim Kashim ya yi wannan gargadin, yayin da ya ke zantawa da manema labarai bayan kammala taron kwamitin tsaro na jihar.

Ibrahim Kashim, ya ce gwamnati za ta tunkari duk wani mai wa’azin da ya yi kalaman da za su iya haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin jama’a, domin ba za su bari wani abu ko maganganun wani su kawo cikas ga zaman lafiyar da ake samu a jihar ba.

Kashim, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Tsaro, ya ce gwamnatin jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, don haka daga yanzu ba za su kyale wani ya ci mutuncin wani ko wasu mutane dangane da imanin su ba.

Leave a Reply