Home Labarai Matasa Sun Jefe Direban Mota Har Lahira a Ondo

Matasa Sun Jefe Direban Mota Har Lahira a Ondo

1
0

Wasu fusatattun matasa sun jefe wani direban mota da
duwatsu har lahira, bisa zargin shi da kashe mutane biyu tare
da raunata wasu shida, a wani hatsari da ya auku a hanyar
Ijoka da ke birnin Akure na Jihar Ondo.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Jihar Ondo SP Olufunmilayo Odunlami-Omisanya, ta shaida wa manema labarai cewa hatsarin ya rutsa da wata mota da wani dan acaba.

Ta ce hatsarin ya yi sanadiyyar mutuwar wani dan acaba, amma maimakon mutanen da ke wurin su taimaka, sai su ka dauki doka a hannun su ta hanyar kashe matashin tare da kone motar sa.

SP Olufunmilayo ta kara da cewa, in da jami’an tsaro ba su isa wurin a kan lokaci ba da abin ya fi haka muni, domin matasan sun yi kokarin kashe iyayen direban, wadanda su ka je wajen da lamarin ya auku don ganin abin da ke faruwa.

Ta ce an tabbatar da mutuwar mutane biyu, yayin da wasu shida su ka samu rauni, kuma a halin yanzu su na samun kulawa a asibiti.