Home Home Mutum 12 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Ebonyi

Mutum 12 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Ebonyi

45
0
Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa, ta tabbatar da mutuwar fasinjoji 12 a wani hatsarin mota da ya auku a Jihar Ebonyi.

Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa, ta tabbatar da mutuwar fasinjoji 12 a wani hatsarin mota da ya auku a Jihar Ebonyi.

Rahotannin sun ce, hatsarin ya auku ne tsakanin wata mota kirar Bas da wata Honda a kan titin Ezillo da ke babbar hanyar Enugu zuwa Abakaliki.

Kwamandar hukumar ta jihar Uche Chukwura, ta ce mutane 14 ne hatsarin ya rutsa da su, inda 12 su ka mutu, biyu kuma su ka samu munanan raunuka.

Ta ce wadanda su ka mutu sun hada da maza 10 da mata biyu, sannan an kai fasinjojin da su ka jikkata asibitin koyarwa na tarayya na Alex-Ekwueme da ke Abakaliki domin yi masu magani.

Leave a Reply