Home Labaru Ilimi Daukar Sojoji: NDA Ta Sanar Da Dalilan Dakatar Da Jarabawar Shiga Kwalejin

Daukar Sojoji: NDA Ta Sanar Da Dalilan Dakatar Da Jarabawar Shiga Kwalejin

758
0

Kwalejin horas da sojoji ta Kaduna NDA ta sanar da cewa, ta dakatar da rubuta jarabawar shiga makarantar ga daliban zango na 71.

Jami’in hulda da jama’a na kwalejin Abubakar ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Kaduna.

Abubakar ya kara da cewa, yanzu an dakatar da jarabawar da aka shirya rubutawa a ranar 13 ga watan Afrelu har sai san sake sanar da wani sabon lokacin rubuta jarabawar.

A karshe kwalejin ta ce zata yi amfani da wannan dama domin sanar da daukacin wadanda suka cike bukatar shiga makarantar a zango na 71 cewa, jarabawar shiga makarantar da aka shirya gudanarwa a ranar 13 ga watan Afrelu 2019 an dakatar da ita.

Leave a Reply