Home Labaru Damfara: ‘Yan Sanda Sun Gurfanar Da ‘Yar Talla Da Laifin Satar Naira...

Damfara: ‘Yan Sanda Sun Gurfanar Da ‘Yar Talla Da Laifin Satar Naira 110, 000 A Legas

560
0

‘Yan sanda sun gurfanar da wata mai talla ‘yar kimanin shekaru 55 mai suna Ademola Tajudeen a gaban kotun Majistare da ke Legas, a bisa zargin ta da satar naira 110,000 a kasuwar Jakande, da ke Ketu a jihar Legas.

Dan sanda mai gabatar da kara, Lucky Ihiehie, ya shaidawa kotun cewa, matar ta saci kudin ne daga wata mata mai suna, Omowunmi Akindulu, wacce take siyar da kayan abinci a Kasuwar.

Ihiehie ya ce, an kai rahoton faruwar lamarin ne a ofishin ‘yan sanda da ke Ketu, sai dai matar ta musanta aikata laifin da ake zargin ta da aikatawa.

Alkalin kotun, Kubeinje, ta bayar da belin wacce ake karan a kan kudi naira 20,000, tare da gabatar da mutum guda da zai tsaya mata a kan wannan kudin, daga bisani kuma aka dage sauraron karan zuwa ranar 25 ga watan Afrilu.

Leave a Reply