Home Labaru Siyasar Sokoto: Gwamna Tambuwal Ya Yi Alkawarin Aiki Da ‘Yan Adawa

Siyasar Sokoto: Gwamna Tambuwal Ya Yi Alkawarin Aiki Da ‘Yan Adawa

544
0

Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya ce a shirye ya ke ya yi aiki tare da abokan adawar sa na jam’iyyar APC domin tabbatar da ci gaban Jihar.

Babban mai taimaka Tambuwal a kan ayyuka na musamman, Yusuf Dingyadi ya bayyana haka a lokacin da yak e zantawa da manema labarai a kaduna.

Tambuwal ya ce wannan lokaci ne na samar da ci-gaba a jihar tunda an kammala zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi, saboda haka ya bukaci abokanan adawar siyasar sa da sauran al’ummar jihar kar su jefa kan su cikin kowace irin fitina, a maimakon haka su garzaya kotunan sauraran kararrakin zabe in har suna da wani korafi.