Home Coronavirus Covid-19: Gwamnati Zata Hana Ma’aikatan Da Basu Yi Rigakafi Ba Zuwa Aiki

Covid-19: Gwamnati Zata Hana Ma’aikatan Da Basu Yi Rigakafi Ba Zuwa Aiki

15
0

Gwamnatin tarayya za ta hana duk wani ma’aikacin gwamnati da bai yi rigakafin korona ba shiga ofis daga ranar 1 ga watan Disamba.


Sakataren Gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin
Shugaban kasa kan yaki da Korona Boss Mustapha ne ya
sanarda hakan yayin zaman da suka yi a nan Abuja.


Boss Mustapha yace ” daga ranar 1 ga watan Disambar 2021,
gwamnatin tarayya za ta bukaci ma’aikatanta su nuna shaidar yin
allurar rigakafi wanda bai wuce sa’o’I 72 ba kafin su shiga
ofisoshin su.”


Yace binciken da suka gudanar makonni hudu da suka gabata ya
nuna cewa yayin da cutar ta covid-19 ke raguwa a wasu jihohi,
tana karuwa ne a wasu jihohin.


Daga karshe kwamitin ya sanar da janye dokar hana shiga
kasashen Afrika ta Kudu da Turkiyya da kuma Brazil.