Home Labaru Yaki Da Ta’addanci: Rundunar Sojan Najeriya Ta Tabbatar Da Mutuwar Shugaban ISWAP...

Yaki Da Ta’addanci: Rundunar Sojan Najeriya Ta Tabbatar Da Mutuwar Shugaban ISWAP Al-Barnawi

12
0

Rundunar sojan Najeriya ta tabbatar da mutuwar Abu Musab al-Barnawi, wanda shi ne shugban ƙungiyar IS na Yammacin Afirka wadda aka fi sani da ISWAP.

]
“Ya mutu kuma zai ci gaba da kasancewa matacce,” a cewar
Hafsan Hafsoshin Tsaro Janar Lucky Irabor.


Sai dai Janar Irabor bai bayar da wani ƙarin bayani ba game da
mutuwar Barnawi, wadda aka fara ruwaitowa a watan Satumba.


Ƙungiyar ta ISWAP ba ta ce komai ba game da lamarin, wadda
ake yi wa kallon ƙungiyar masu iƙirarin jihadi mafi ƙarfi a
Najeriya tun bayan mutuwar shugaban Boko Haram Abubakar
Shekau a farkon wannan shekarar.


Bayan haka ne kuma mayaƙan Boko Haram ɗin suka dinga miƙa
wuya ga ISWAP da kuma sojojin Najeriya.