Home Labaru Adesina Ya Ce Yadda Kudan Zuma Ke Bin Zuma Haka Jama’A Ke...

Adesina Ya Ce Yadda Kudan Zuma Ke Bin Zuma Haka Jama’A Ke Bin Shugaba Buhari

11
0

Mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari, dan siyasa ne da yake da farin jinin da ya kai ga mutane na binshi kamar yadda kudan zuma ke bin zuma domin so da kauna, wanda a tarihin Najeriya ba wani dan siyasa da yake raye ko wanda ya mutu da yake da wannan farin jinni.

Femi Adesina, ya yi wa shugaban kasa wannan koɗa da yabo ne a wata maƙala da ya rubuta wadda ya saba yi a duk mako, wadda kuma kamar maimaici ne na irin kalaman da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya yi a lokacin da yake jawabi ga jami’an diflomasiyya a ofishin jakadancin Najeriyar a London, a makon da ya gabata.

Adesina ya ce yadda mutane ke tururuwa domin halartar duk inda Shugaba Buhari yake, ko fitattun ƴan siyasa irin su Dr Nnamdi Azikiwe da Cif Obafemi Awolowo da Mallam Aminu Kano ba su kai shi ba, duk kuwa da cewa su shugabanni ne da suka yi farin jini tare da yi wa Najeriya hidima kuma suke da magoya baya da har yanzu ake martaba su.

Makalar ta Adesina wadda kusan tambihi ne na bayanan da Farrfesa Osinbajo ya yi na yabo da koda Buhari, ya ce duk kalaman da Osinbajo ya yi a wancan jawabi na London haka suke, domin shi ma mutum ne mai gaskiya.