Home Labarai Yashe Tashoshi Jiragen Ruwa: NPA Ta Kashe Fiye Da Dala Miliyan 200...

Yashe Tashoshi Jiragen Ruwa: NPA Ta Kashe Fiye Da Dala Miliyan 200 A Legas

99
0
Bello Koko
Bello Koko

Bayani ya nuna cewa, Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya NPA ta kashe fiye da Dala Miliyan 200 wajen aikin yashe hanyoyin teku da suka hada tashoshin jiiragen ruwan da ke yankin Legas gaba daya LPC da suka hada da tashar ‘Tin-Can Island Port’, da ‘Roro Port’ da kuma tashar kwantaina a cikin shekara 10 da suka wuce.

NPA, na kashe kimanin dala miliyan 2.6 a duk shekara wajen yi wannan aikin, kamar yadda bayanin ya nuna.

Wani jami’in ma’aikatar tattallin arzikin teku ya bayyana cewa, da farko ana kashe dala miliyan 3.71 ne a shekara amma daga baya aka kara kudaden saboda bukatar a fadada aikin da ake yi na yashe tekun don manyan jiragen ruwa su samu jin dadin zirga-zirga ba tare da matsala ba da kuma bukatar samar da irin yanayin da ake samu a wasu tashoshin jiragen ruwa na duniya.

A nasa tsokacin Shugaban NPA, Alhaji Muhammed Bello-Koko, ya bayyana cewa, hukumar ta samar da kayan aiki na zamani domin tattara kudaden haraji daga jiragen ruwa da amsu hulda da tashosgin a cikin sauki, hakan ya taimakwa wajen kara yawan harajin da hukumar ke samu a ‘yan shekarun nan.

Masu ruwa da tsaki a bangaren harkokin tashoshin jiragen ruwa sun yaba da kokari da hangen nesa na shugaban NPA Muhammad Bello koko, musamman yadda ya fito da sabbin hanyoyin kara samar da kudasden shiga wanda hakan ya taimaka wajen kara yawan kudin da ke shiga asusun gwamnatin tarayya.

Leave a Reply