Home Labarai Halasta Kuɗin Haram: Kotu Ta Yi Watsi Da Tuhumar Da Ake Yi...

Halasta Kuɗin Haram: Kotu Ta Yi Watsi Da Tuhumar Da Ake Yi Wa Adoke

42
0
images (49)
images (49)

Mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya a nan Abuja ya yi fatali da tuhumar halasta kuɗin haram da hukumar EFCC take yi wa tsohon atoni janar na Najeriya, Mohammed Adoke.

Da yake yanke hukunci kan ƙarar da tsohon babban jami’in ya shigar ta neman a soke ƙarar, alƙali Ekwo ya ce EFCC ta gaza gabatar da shaida kan Adoke.

EFCC ta tuhumi Adoke da Abubakar Aliyu, wani mai harkar gine-gine ne a 2017, da almundahana ta naira miliyan 300.

Alƙali Ekwo ya kori ƙarar tare da wanke shi.

Sai dai alkali Ekwo ya yanke cewa Aliyu Abubakar, mutum na biyu da ake ƙara, dole ya nemi shaida saboda akwai zarge-zargen da ya kamata ya kare kan sa.

Leave a Reply