Home Labaru Kasuwanci Baje Kolin Motoci Na Afirka: Shirye-Shiryen Gudanar Da Biki A Watan Mayu...

Baje Kolin Motoci Na Afirka: Shirye-Shiryen Gudanar Da Biki A Watan Mayu A Legas Ya Kammala

31
0
Luqman Mamudu
Luqman Mamudu

A halin yanzu an kammala shirye-shieyen bude bikin baje kolin motoci na yankin Afrika ta yamma karo na 4 da za a gudanar a ranar 14 zuwa 16 ga watan Mayu, na wannan shekarar a cibiyar Landmark dake Victoria Island, a Legas.

 Ana sa ran masu baje koli fiye da 250 za su shiga shirin ana kuma sa ran za a samu mahalarta taron fiye 4,500 da za su zo daga sassan duniya.

Taron baje kolin zai gudana ne a karkashin jagorancin shugaban hukumar samar da motoci ta kasa, Lukman Mamudu.

A jawabin sa, ya bayyana cewa, taron baje kolin zai samar wa masu ruwa da tsaki a sashin damar tallata hajojin su da kuma tattaunawa da gamnatocin yankin Arfika ta yamma a kan yadda za su ci gajiyar juna a fannin samar da motoci masu saukin kudi da kuma motoci  masu amfani da iskar gas da kuma masu amfani da wutar lantarki musamman ganin ana yekuwar kauce wa amfani da man fetuur saboda yadda hayakin ke cutar da muhalli.

Lukman Mamudu ya kuma ce sanin dokoki da ka’idojin gudanar da taron baje kolin zai taimaka wa masu halartar taron fahimmtar yadda za su zuba jari a bangaren da za su samu ribar da ya kamata, musamman a wannan lokaciin da ake karfafa gudanar da kasuwanci a tsakanin kasashen yankin Afrika ta yamma da ma yankin Afrika gaba daya.

Leave a Reply