Home Labaru Takaddama: Magu Ya Musanta Rahotannin Da Ke Danganta Shi Da Rashawa

Takaddama: Magu Ya Musanta Rahotannin Da Ke Danganta Shi Da Rashawa

329
0

Tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa Ibrahin Magu, ya sake rubuta wata wasika zuwa ga kwamitin bincike a karkashin Mai Shari’a Ayo Salami, ya na mai musanta rahotannin da kafafen yada labarai su ka yada da ke danganta shi da rashawa yayin da ya ke tsare.

Tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa Ibrahin Magu

Ibrahim Magu ya kuma zargi kwamitin binciken da kin ba shi isasshen lokaci da damar kare kan sa.

 A cikin wasikar, Magu ya ce kwamitin bai ba shi wasikar da ke kunshe da zarge-zargen da ake yi ma shi wadda ke da nasaba da rashawa ba, da kuma rahoton binciken da aka gudanar game da kadarorin da hukumar EFCC ta kwato.

Kwamitin dai ya na binciken Magu ne bisa zargin rashawa da rashin biyayya ga na gaba da shi kamar yadda ministan shari’a Abubakar Malami ya shigar da koke.

Leave a Reply