Home Labaru Rikicin Kauru: Ku Fallasa Duk Wanda Ku Ka San Ya Na Da...

Rikicin Kauru: Ku Fallasa Duk Wanda Ku Ka San Ya Na Da Hannu A Ciki – El-Rufa’i

274
0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmad El-Rufai, ya bukaci shugabannin Zangon Kataf da Kauru su fallasa duk wadanda su ka sani da hannu a rikicin yankunan biyu da ba su jituwa da juna, lamarin da ke kara haddasa asarar rayuka da dukiyoyin al’umma.

El-Rufai ya bayyana haka ne, yayin wani taro da ya yi da masu rike da mukaman siyasa da sarakunan gargajiya, inda ya bukaci su fallasa duk wadanda su ka san su na janyo rikici a yankunan.

 A cikin wata sanarwa da mai ba gwamnan shawara ta fuskar yada labarai Muyiwa Adekeye ya fitar, gwamnan ya ce ya rage ga masu ruwa da tsaki na yankunan su bude baki su bayyana abin da ke faruwa.

 An dai gudanar da taron ne tare da jami’an tsaro da sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki daga yankunan a matsayin hanyar dakile rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a yankunan.

El-Rufai ya ce abin da su ke gani a yanzu shi ne, babu tsaro a yankunan kudancin Kaduna, lamarin da ya kwatanta da babbar barazana ga ci-gaban yankin.