Home Labaru SABON HARI: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 7 A Jihar Katsina

SABON HARI: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 7 A Jihar Katsina

1510
0

Rahotanni daga jihar Katsina na cewa, akalla mutane bakwai sun rasa rayukan su, bayan wani mumunan hari da ‘yan bindiga su ka kai a kauyukan Kasai da Nahuta da ke karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

Wani mazaunin kauyen Kurmiyal da ke makwaftaka da kauyukan da lamarin ya faru ya shaida wa manema labarai cewa, ‘yan ta’addan sun afka wa kauyukan ne a da misalin karfe 7 na daren Juma’ar da ta gabata, yayin da jama’a ke shirin fara Sallar Magariba.

Wata majiya ta ce duk da cewa hukumar ‘yan sanda ba ta tabbatar da harin ba, amma a kauyen Kasai kadai an kashe mutane biyu, sannan an kashe mutane biyar a kauyen, baya ga wadanda su ka jikatta da dama.

Majiyar ta cigaba da cewa, ‘yan bindigar rike da bindigogi sun fara harbin Kan-Mai-Uwa-Da-Wabi domin fatattakar mutane.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Katsina SP Gambo Isah, ya ce ba ya da masaniya game da faruwar lamarin, amma zai tuntubi na kusa da yankunan da lamarin ya faru.