Home Labarai Tabbatar Da Nasarar Deby: Firaiministan Chadi Ya Ajiye Aikin Sa

Tabbatar Da Nasarar Deby: Firaiministan Chadi Ya Ajiye Aikin Sa

67
0
Chads Newest Leader Succes Masra Gives Up His Salary News Central TV 1
Chads Newest Leader Succes Masra Gives Up His Salary News Central TV 1

Firaiministan Chadi, ya miƙa takardar murabus bayan da aka tabbatar da nasarar sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙasar,

Mahamat Idriss Deby a zaɓen da aka yi na ranar 6 ga watan Mayun 2024.

An dai naɗa Masra ne a matsayin firaiminista a gwamnatin rikon kwarya domin kyautatawa masu hamayya da juyin mulkin da aka yi a 2021.

A watan Maris ne dai hukumar zaɓen ƙasar ta amince da takarar mista Masra a matsayin ɗan takarar shugabancin ƙasar da zai fafata da Mahamat Deby.

To sai dai tun dai kafin sanar da sakamakon zaɓen na farko-farko, Masra ya ce shi ne ya lashe zaɓen, inda ya ce an tafka maguɗi.

Hukumar Zaɓen Chadi ta ce Deby ya lashe zaɓen ne da kaso 61 na dukkan ƙuri’un da aka kaɗa saboda shi ne ya yi nasara.

Sai dai kuma Masra wanda ya yi takarar da Deby ya yarda abin da hukumar ta ayyana bisa cewa babu wata damar da ta rage masa da kin amince wa da sakamakon.

a shafinsa na X ya ce bisa tsarin kundin mulki, yau ya miƙa takardar murabus da kuma ta gwamnatin rikon kwarya wadda ta zama tamkar ba ta da mfani bayan zaɓen ranar 6 ga watan Mayu.

Leave a Reply