Ƴan wasan Barcelona biyu Joao Cancelo da Joao Felix suna cikin wadanda Portugal ta gayyata a gasar Euro 2024
Haka kuma tawagar Jamus ta gayyaci Ter Stegen da Ilkay Gundogan da kuma ta Faransa da ta kira Kounde, domin buga wasan da za a fara cikin watan Gobe.
Tuni dai tawagan da suka samu gurbin shiga gasar da za a fara daga 14 ga watan Yuni, suke sanar da ƴan ƙwallon da za su buga musu gasar ta Euro 2024.
Koci, Roberto Martinez ya bayyana Cancelo da Felix cikin ƴan ƙwallo 26 da za su buga wa Portugal babbar gasar tamaula ta nahiyar Turai.














































