Rishi Sunak ya sanar da cewa zai rushe majalisar zatarwar ƙasar a mako mai zuwa gabanin zaɓen da za a gudanar a ranar huɗu ga watan Yuli.
Hakan na zuwa ne kwana guda bayan cece-ku-ce da raɗe-raɗin da aka riƙa yi,
bayan hauhawar farashi a ƙasar ta kai wani mataki da ba ta taɓa kaiwa ba cikin shekara uku.
Jam’iyyar da ke mulkin ƙasar ta ƴan mazan jiya za ta shiga zaɓen yayin da take baya a ƙuri’ar jin ra’ayin al’umma, yayin da jam’iyyar Labour take gaba.
Jam’iyyar Conservatives ta kwashe shekara 14 a jere tana jagorancin ƙasar ta Birtaniya.