Home Labaru Ta’addanci: Hukumar NDLEA Ta Koka Kan Yadda Ake Kashe Mata Jami’an Ta

Ta’addanci: Hukumar NDLEA Ta Koka Kan Yadda Ake Kashe Mata Jami’an Ta

330
0

Hukumar kula da abinci da magunguna ta kasa NDLEA za ta dauki mataki a kan hare-haren ta’addancin da a ke kai wa jami’an ta na ba gaira ba dalili.

Shugaban kula da harkokin kiwon lafiya na hukumar, Muhammad Abdullah ya bayyana haka tra bakin jami’in yada labarai na hukumar Jonahy Achema a lokacin wani taron sanin makamar aiki da ya gyudana a Abuja.

Abdullahi ya kara da cewa, jami’an su na fuskantar barazana daga bangaren wasu ‘yan ta’adda da basu son zaman lafiya, inda ya ce kawo yanzu an kashe masu jami’ai kimanin 200 tun lokacin da aka kafa hukumar.

Muhammad Abdullahi ya ci-gaba da cewa, an kai hari a kan ma’aikatan hukumar NDLEA a jihar Ondo wanda ya haddasa mutuwar jami’an su a hudu, a cikin watan Fabrairu shekara ta 2019.

Shugaban ya ce binciken da hukumar ta yi ya nuna cewa, har yanzu jami’an su na fuskantar barazana daga wajen ‘yan ta’addan, Saboda haka su ka bukaci masu ruwa da tsaki da gwamnatoci su sa ido a kan faruwar irin wannan Lamarin da ke shafar ma’aikatan su, tare da daukar matakin da ya dace a kan duk wanda aka kama da laifi.

Leave a Reply